Jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Isa A. Isa, ya yi martani akan daure Sadiya Haruna da kotu ta yi, cewa Allah ne ya tabbatar da gaskiyarsa.
Isa A Isa ya ce, shiyasa kotu ta daure jarumar na wata shida bayan ta same ta da hannu dumu-dumu a tuhumar da ake mata na masa batanci.
Ya kuma ce, tun farko abun da ya hadasa da jarumar taimako ne sabanin kazafin da ta yi masa na cewa sun yi auren mutu’a da shi.