Dan wasan gaba na Tottenham, Harry Kane ne ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da suka tashi 2-2 da Chelsea ranar Lahadi.
Emile Hojbjer ya soke kwallon da Kalidou Koulibaly ya ci, kafin Reece James ya dawo da ragamar Blues.
Ita ce kwallo ta 184 da kyaftin din Ingila ya ci a Spurs, wanda hakan ya sa ya zama dan wasan da ya fi yawan kwallaye a haduwa guda a tarihin gasar Premier, inda ya yi daidai da yawan kwallayen da Sergio Aguero ya ci wa Manchester City.
Kane kuma ya zura kwallaye 42 a wasannin derby na London a gasar.
Wannan ne ya sanya shi ci daya kacal a bayan fitaccen dan wasan Arsenal, Thierry Henry.


