Kaftin ɗin tawagar Ingila, mai taka leda Bayern Munich, Harry Kane ya kafa tarihin cin kwallo 50 cikin wasannin ƙalilan a babbar gasar tamola ta Jamus.
Dan wasan gaban ya ci ƙwallo uku rigis a wasan da Bayern Munich ta doke Augsburg da ci uku da nema a ranar Juma’a a Bundesliga a wasansa na 43 da ya buga wa ƙungiyar a gasar.
Da wannan bajinta Kane ya goge tarihin da Erling Halland ya kafa na cin wallo 50 a wasa 50 da ya buga wa Borussia Dortmund.
A shekarar da ta gabata ne Bayern ta sayi Kane daga Tottenham Hotspur ta Ingila kan kuɗi dala miliyan 150, wani abu da bai yi wa da dama daga cikin magoya bayan Hotspur daɗi ba.