Kamfanonin samar da wutar lantarki, sun ce suna iya dakatar da ayyukansu na samar da wuta saboda tarin bashin da ya haura naira tiriliyan 5.2 da har yanzu gwamnati ba ta biya su ba, wanda ke barazana ga cigaban aikinsu na samar da lantarki a ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da lantarkin, Dr. Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun jima suna nuna kishin kasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji.
Ta ce akwai sabon bashi da ya kai naira tiriliyan 1.2 daga wutar da aka samar a farkon rabin shekarar 2025, wanda ya ƙaru kan bashin da suke bin gwamnati zuwa naira tiriliyan 5.2.
Wannan ya haɗa da naira tiriliyan 2 daga shekarar 2024 da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 da ya kai naira tiriliyan 1.9.
A cewarta, “Kuɗin da ake kashewa wajen samar da wuta a kowane wata yana kai wa naira biliyan 250, amma gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 900 kacal a kasafin kuɗin 2025, kuma har zuwa yau ba a samu cikakken tabbacin samun wannan kuɗi ba.”.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce “gwamnati na ƙoƙarin rage wani bangare na bashin, amma ba a bayyana yadda hakan zai faru ba.