Ƙungiyar masu kamfanonin samar da kayayyaki a Najeriya, MAN, ta ce kamfanoni kusan dari uku ne suka durƙushe tun bayan da aka fara samun karyewar darajar kuɗinƙasar, Naira.
Karyewar darajar naira dai ta jefa tattalin arzikin Najeriya cikin wani hali, lamarin da masu masana’antun ke cewa suma basu tsira ba.
Alhaji Sani Hussaini mamba a majalisar zartarwa a ƙugiyar kamfanoni a Najeriya, ya ce faɗuwar darajar naira ta kai ga tashin sama da kashi ɗari na abubuwan da suke sarrarafawa.
Kuma ba za su iya ƙara farashin kayyakinsu ya kai wannan farashinba a kasuwa.
Haka zalika kayan abinci su ne suka fi tafiya a kasuwa, lamarin da ya sa idan ba su kamfani ke sarrafawa ba, kasuwarsa na ci baya.
Inda ya ce kashi 80 cikin ɗari na kayyakin da kamfanonin ke amfani da su shigo da su a keyi daga waje.
Lamarin da ya ce ya jefa wasu ƙarin kamfanoni kimanin 150 cikin tangal-tangal.
Daidaituwar farashin kuɗaɗen waje, musamman dalar Amurka, a cewarsa zai taimaka gaya wajen tafiyar da ayyukan kamfanoni da masana’antu a ƙasar.
Tun bayan bullo da garambawul ta fuskokin da suka haɗa da janye tallafin man fetur da daidaita kasuwar musayar kuɗaɗen wajen a bara ne, ƙasar ta shiga wani hali.
Yayin da al’ummarta ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa.