fidelitybank

Kamfanin wutar lantarki ya yi barzanar yanke wuta a fadar Tinubu

Date:

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja AEDC ya yi barazanar katse wutar lantarki a fadar shugaban Najeriya da na wasu ma’aikatun gwamnati 86 a kan bashin kuɗin wuta sama da naira biliyan 47 da yake bin su.

Wasu daga cikin ma’aikatun da barazanar ta shafa sun haɗa da ma’aikatar kuɗi da ta yaɗa labarai da ta kasafin kuɗi da ta ayyuka da gidaje, da gwamnan CBN da ofishin Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da sauran su.

A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, AEDC ɗin ya bai wa ma’aikatu da ofisoshin na gwamnati kwana 10 domin biyan basukan ko kuma a yanke musu lantarki, wato daga 28 ga watan Fabarairun 2024.

Bangaren samar da wutar lantarki a Najeriya dai ya shafe shekaru yana fama da matsalar bashi.

A makon da ya gabata ne Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da su tashi tsaye idan ba haka ba duk wanda aka samu da laifi, za a soke lasisin sa.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp