Kamfanin man fetur na kasa NNPCL, ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar nan.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari, ya ce an ɗauki matakin ne da zimmar haɓaka yawan man da ake haƙowa, yana mai cewa bincike ya nuna Najeriya za ta iya haƙo fiye da ganga miliyan biyu duk rana.
Ya ce, an ayyana yaƙi ne a kan ƙalubalen da ake fuskanta a harkokin haƙo fetur.
Mele Kyari da yake magana a taron masu ruwa da tsaki a harkar mai ta kasa a yau Talata a Abuja, ya ce, sun shaida wa abokan hulɗar su, cewa akwai isashen kayan aikin hakan man.
Ya ƙara da cewa, yaƙin zai taimaka wa NNPCL da abokan hulɗarsa na kawo ƙarshen duka matsalolin, domin cigaba da haƙowa da sayar da man ba tare da tsaiko ba.
Da yake magana kan motoci amfani da iskar gas na CNG, Kyari ya ce tuni kamfanin ya gina tashoshin iskar gas na CNG, inda za su ƙaddamar da 12 daga ciki a Legas ranar Alhamis mai zuwa.