Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da dadewa ba, za ta tilasta wa kamfanonin jiragen sama su fara biyan diyya ga fasinjoji saboda jinkiri ko soke tashi jirgi, matuƙar ba wani al’amari ne daga Allah ya haddasa matsala ba.
Gidan talbijin na Channels ya ambato ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo na bayyana haka lokacin da yake ganawa da kamfanonin jiragen sama a Abuja ranar Litinin.
“Dangane da jinkiri ko soke tashin jirgin sama, ina so na tabbatarwa al’ummar Najeriya da ke korafi a kullum game da irin wannan matsalar, za mu fara aiwatar da tanade-tanaden dokar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya’ wadanda ‘yan Najeriya ba su san da su ba,”
“Wannan tanadi shi ne kamfanonin jiragen sama za su biya diyya a kan jinkiri ko soke tashin jirgi, matuƙar ba wata matsala ce ta faru sanadin wani al’amari daga Allah ba.
“Amma idan wani al’amari ne daga Allah, babu wata diyya da za su biya.”
Sai dai Keyamo ya bukaci ma’aikatan kamfanonin jiragen sama su samar da hanyoyin sadarwa tabbatattu da ke bai wa fasinjoji damar samun bayanai a kan jinkiri ko sokewar tashin jiragen sama.