Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, da ‘yan ƙasar sun san irin halin matsi da takwarorinsu na ƙasashen Afirka ke ciki da sun gode wa Allah.
A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban ya fadi hakan ne ranar Asabar lokacin da ya kai wa Sarkin Katsina Dr Abdulmumini Kabir Usman ziyara a fadarsa.
Ya kara da cewa ”Muna kira ga mutane da su yawaita haƙuri, muna iya bakin ƙoƙarinmu. Babu abin da ya fi zaman lafiya, muna roƙon Allah ya ba mu damar ganin bayan masu ƙoƙarin wargaza mana zaman lafiyar ƙasarmu.”
Shugaban ya kuma ce, zai ci gaba da yin bakin ƙoƙarinsa wajen yalwata wa ‘yan kasar bayan jin ƙorafe-ƙorafe kan halin da ‘yan ƙasar ke ciki daga bakunan gwamnan jihar Aminu Bello Masari da kuma Sarkin Katsina.
”Da mutanenmu sun san irin halin matsin rayuwa da wasu ƙasashen Afirka ke ciki a halin yanzu, da sun gode wa Allah game da halin da suke ciki a ƙasar nan,” in ji Shugaban na Najeriya.