Tsohon shugaban tsagerun Neja-Delta kuma wanda ya kafa rusasshiyar kungiyar Neja Delta People Volunteer Force (NDPVF), Mujahid Asari-Dokubo, ya sake yi wa dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar Labour (LP), Peter Obi zagon kasa, yana mai cewa, ya kamata tsohon gwamnan jihar Anambra ya kasance a gidan yari maimakon ya tsaya takarar shugaban kasa.
Dokubo wanda bai yi kasa a gwiwa ba wajen sukar Obi tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a matsayi na daya a kasar, a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta a daren Lahadi, ya ce, mai rike da tutar jamâiyyar LP ya kasance a gidan yari saboda ya zuba kudaden gwamnatin jihar Anambra a harkokin kasuwancinsa na kashin kansa a lokacin yana gwamna.
âA wata kasa ta alâada, Peter Obi ya kamata ya kasance a gidan yari saboda saka hannun jari a cikin kasuwancin iyali kuma ya gaza. Bai kamata ya tsaya takarar Shugaban kasa ba,â
AÂ âyan makonnin da suka gabata, Asari-Dokubo ya rika zage-zage a kan Obi a tafuska daban-daban, inda ya yi watsi da nasarorin da tsohon gwamnan ya samu, yana mai cewa duk karya ce.
Ripples Nigeria ta ba da rahoton wani harin da tsohon dan ta’addan ya kai inda ya kira Obi a matsayin dan damfara a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu.
âAkwai dan damfara a garin. Peter Obi yana damfarar mutane da karya kuma mutane suna gaskata shi.