fidelitybank

Kamata ya yi Facebook ya dakatar da gwamnatin Najeriya – Lauyan Kanu

Date:

Lauyan kasar Amurka, Bruce Fein, wanda ya ke kare Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, ya bukaci Facebook da ya haramtawa gwamnatin Najeriya.

A cewarsa, ya kamata Facebook ya yi la’akari da sanya takunkumi ga gwamnatin Najeriya, bisa zargin kisan kiyashi da cin zarafin bil’adama da ake yi wa kungiyar IPOB da al’ummar yankin kudu maso gabas.

Daily Post ta rawaito cewa, roko na sa ya biyo bayan kiran da Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu ya yi, na neman Facebook ta haramtawa kungiyar IPOB amfani da kafafen sada zumunta.

Mohammed ya ce, Facebook bai taka rawar gani ba wajen hana kungiyar IPOB tada zaune tsaye ta hanyar amfani da dandalin.

Fein a cikin wata wasika da ya aike wa Mark Zuckerberg, wanda ya kafa Facebook ya ce, “Ina sane da yadda gwamnatin Najeriya ta yi kakkausar suka ga Facebook na haramta kungiyar IPOB da mambobinta daga dandalin sada zumunta bisa zargin tayar da rikici. Wannan yunƙurin dai na nuni ne kan matakin gwamnatin Najeriya na haramta kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci a watan Satumban 2017. Dukkan labarin ya kara bayyana.

“Tsarin dokar ya sabawa tsarin da ya dace. An hana IPOB sanarwar da kuma damar mayar da martani. Wannan haramcin shi ne rashin gaskiya ipse dixit na shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

“Saboda haka, ina rokon a cikin girmamawa da Facebook ya tsawata wa gwamnatin Najeriya da ke karkashin mulkin Fulani saboda neman tauye hakkin ‘yan kungiyar ta IPOB.

latest news nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp