Wani jigo a jamâiyyar APC a jihar Ribas, Kingsley Wenenda Wali, ya yi kira da a yi sulhu na gaskiya a tsakanin shugabannin jihar, ta yadda za a jawo ci gaban jihar da ake bukata.
Ya ce, sulhun bai kamata ya kasance tsakanin tsohon Ministan Sufuri, Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi da Gwamna Nyesom Ezenwo Wike, amma ga kowane dan jihar.
Wali, wanda kuma shi ne shugaban wata kungiya mai fafutukar tabbatar da shugabanci na gari, Unity House Foundation (UHF), ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook da aka tabbatar.
Jigon na APC ya yi kira ga Wike da ya dauki matakin farko wajen sasantawa ta hanyar sakin dan takarar gwamna da aka tsare a jamâiyyar PDP kuma dan majalisar wakilai, Hon. Farah Dagogo.