Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye, ya ce, ya kamata a jefe masu neman jinsi abin da a cewarsa yin hakan ba zai zama laifi ba.
A wani taron ƴan jarida ranar Juma’a, yayin da yake mayar da martani game da tambayar da wani ɗan jarida ya yi masa ya ce Burundi ba ta buƙatar agajin manyan ƙasashe masu ƙarfin iko su “su ajiye taimakonsu” idan har yin hakan na tare da buƙatar neman a bai wa masu neman jinsi dama.
A jawabin nasa, shugaban ya yi misali da Injila inda ya ce Ubangiji ya yi hani da neman jinsi inda ya ce neman jinsi sam ba batu bane a Burundi.
“A wurina, ina ganin idan muka ga masu irin wannan aƙida a Burundi, a kai su filin wasa a jefe su, kuma yin hakan ba zai zama laifi ba,” kamar yadda shugaban ƙasar ta Burundi ya ce.
Mr Ndayishimiye ya ce neman jinsi kamar yin zaɓi na tsakanin shaiɗan da Ubangiji”.
“Idan kana son zaɓar Shaiɗan, toh ka je ka yi rayuwa a irin ƙasashen kuma ina tunanin masu fafutukar zuwa can suna son rungumar ɗabi’un, ya kamata su tsaya a can kada su kuskura su kawo mana su.” in ji shugaban.
Burundi dai ta haramta neman jinsi kuma laifi ne da ke iya janyo hukuncin kusan shekara biyu a gidan yari.
A watan Agusta, mutum bakwai aka yankewa hukuncin shekara tsakanin daya zuwa biyu a gidan yari bayan da kotu a Gitega ta same su da laifin neman jinsi tuhumar da suka musanta.


