Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ta zama ‘yar takarar shugaban Amurka ƙarƙashin jam’iyyar Democrats a hukumance.
Yayin da take jawabi ta wayar tarho, Ms Harris ta ce ”ta samu alfarmar zama ‘yar takara”, yayin da take ci gaba da samun goyon baya gabanin babban taron jam’iyyar da za a gudanar nan gaba cikin wannan wata a birnin Chicago.
Ms Harris ce mace baƙar fata ta farko kuma ‘yar asalin kudancin Asiya ta za ta yi takarar shugabancin Amurka a ƙarƙashin ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun ƙasar.
Idan har ta doke Donald Trump – ɗan takarar jam’iyyar Republican, a zaɓen watan Nuwamba da ke tafe – za ta kasance mace ta farko da ta shugabanci Amurka.