Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa, Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta zaɓi gwamnan Minnesota Tim Walz a matsayin wanda zai mara mata baya a zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba.
Ana sa ran za ta yi sanarwa a hukumance game da hakan nan ba da jimawa ba.
Rahotanni sun ce zaɓi ne na hikima saboda mutum ne da yake da ɗabi’un da ake nema.
Mista Walz shi ne mutumin da ya kira haɗin Donald Trump da mutumin da zai yi masa mataimaki, JD Vance a matsayin bambarakwai.
Masu sharhi sun ce ta zaɓi gwamna Walz domin ƙara faɗaɗa goyon bayan jam’iyyar Dimokrats tsakanin fararen fata mazauna yankunan karkara.
Ƙuri’ar jin ra’ayi ta nuna cewa Kamala ta cike giɓin da ke akwai tsakaninta da Trump tun da Shugaba Biden ya janye daga takarar a watan da ya gabata.