Mataimakiyar shugabar Amurka, Kamala Harris ta bayyana manufofinta na abin da za ta yi a ranar farko idan ta zama shugabar ƙasar.
Ta bayyana hakan ne a hirarta ta farko tun bayan maye gurbin Joe Biden a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar Democrat.
Kafar Talabijin ta CNN ce ta gabatar tattaunawar da aka riga aka naɗa wadda ta yi tare da abokin takararta Tim Walz.
Da farko ta ki faɗar abin da za ta yi a ranar farko idan ta zama shugabar Amurka, inda ta fi mayar da hankali kan batun rage tsadar kayayyakin masarufi.
Ms Harris ta kuma ce za ta naɗa yan jam’iyyar Republican a majalisar ministocinta. Donald Trump dai ya yi watsi da hirar wadda ya kira ‘marar daɗin ji’.