Ƴar takarar shugaban ƙasar Amurka a Jami’yyar Democrat, Kamala Harris, ta kalubalanci abokin hamayyarta Donald Trump na Jam’iyyar Republican da ya tabbatar da cewa, yana da ƙoshin lafiyar da zai iya tafiyar da aikin ofishin shugaban ƙasa.
Harris na magana ne bayan fadar White House ta fitar da wata takarda daga likitanta wanda ke nuna cewa tana cikin koshin lafiya.
A nasa ɓangaren a wani gangamin da ya yi a California, Mista Trump ya sake zaƙe wa kan batun ƴan ci-rani, inda ya zargi ‘yan jam’iyyar Democrat da shigo da abin da ya kira “Rundunar masu aikata laifuka a ƙasar.
Trump ya ce duk wanda zai shigo da gungun masu aikata laifuka domin su mamaye Amurka bai cancanci ya yi takarar shugabancin ƙasar ba.