Ɗan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican, Donald Trump ya caccaki Kamala Harris da ake kyautata zaton za ta zama ‘yar takarar jam’iyyar demokrats a wajen taron kiristoci masu ra’ayin riƙau.
Yayin da yke jawabi a wajen taron a jihar Florida, mista Trump ya bayyana wadda alamu ke nuna za ta zama abokiyar karawarsa a zaɓen watan Nuwamba da cewa ba ta cancanta ba.
Ya ce a matsayinta ta mataimakiyar shugaban ƙasa ”a gwamnatin da ta gaza” – ta kasa taɓuka komai, inda miliyoyin baƙin haure suka tsallaka kan iyaka.
Ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa goyon bayan da Trump ke samu ya ragu, tun bayan janyewar Joe Biden tare da mara wa Kamala Harris baya a makon da ya gabata.


