Tsohon ɗantakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da EFCC ta yi na da alaƙa shigarsa cikin haɗakar jam’iyyun hamayya.
Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da yunƙurin cin zarafi da tsoratarwa da nufin murƙushe jam’iyyun hamayya a ƙasar.
“Abun da muke gani a yanzu shi ne yadda gwamnatin Tinubu ke amfani da yaƙi da cin hanci a matsayin karen farauta domin daƙile jagororin jam’iyyun hamayya tare da jan su zuwa jam’iyya mai mulki.”
Ya ce abin da ke faruwa ba ya cikin, “manufarmu a lokacin da muka yi aiki tuƙuru domin assasa hukumar EFCC. Yanzu abubuwa na fitowa fili cewa duk wani ɗansiyasa da ke da alaƙa da jam’iyyun adawa yana fuskantar barazanar zargin cin hanci da rashawa, amma da zarar sun koma jam’iyya mai mulki, sai a ‘yafe’ musu.”
Atiku ya ce duk da cewa yaƙi da cin hanci da rashawa lamari ne da ke buƙatar goyon bayan ƴan Najeriya, ya ce haɗa yaƙin da wata manufa ta daban abu ne da ya cancanci suka daga ƙungiyoyi gwagwarmaya da ma ƙasashen duniya masu ƙawance da Najeriya.
A ƙarshe Atiku ya ce yana ba ƴan Najeriya tabbacin cewa za ba su yi shiru su zura ido suna gani ana ɗaukar matakai da suke barazana ga dimukuraɗiyyar ƙasar ba, wadda ya ce ana yunƙurin mayar da ita siyasar jam’iyya ɗaya.