fidelitybank

Kama Dan Jarida Daniel a Najeriya tauye hakkinsa ne – Kungiyar kare hakkin bil adama

Date:

Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta ce tsare ɗan jaridar nan a Najeriya, Daniel Ojukwu ya take ƴancinsa a matsayin mai bayar da rahoto.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar wadda ta aike wa kafafen yaɗa labarai a Najeriya.

HRW ta nemi hukumomin Najeriya su gaggauta sakin Ojukwu idan ba a tuhume shi da aikata babban laifi ba.

A cewar ƙungiyar, ƴan jarida da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama a Najeriya na zanga-zanga kan kama Daniel Ojukwu tare da tsare shi.

Ɗan jaridar da ke aiki a gidauniyar aikin jarida na bin diddigi, ya ɓata ne a ranar 1 ga watan Mayu. Daga bisani kuma an gano cewa yana hannun ƴan sanda, inda aka zarge shi da take dokar yaƙi da laifukan intanet ta Najeriya.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa hukumomi sun yi ta watangaririya da shi a tsakanin ofisoshin ƴan sanda har da cibiyar daƙile laifukan intanet da sashen binciken manyan laifuka a Abuja.

HWR ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ta yi tanadi cewa duk wanda ake zargi da aikata laifi a gurfanar da shi a gaban kotu cikin sa’a 48 da aka kama shi.

Ƙungiyar ta ce “Ojukwu ya ci gaba da zama a tsare ba tare da tuhumarsa ba fiye da kwana tara.”

Wurin aikin Ojukwu ya ce an kama ɗan jaridar ne kan wani rahoto da ya yi wanda aka wallafa a watan Nuwamba, inda ya zargi wani tsohon babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan shirin tabbatar da muradun ƙarni, Adejoke Orelope-Adefulire, da tura naira miliyan 147 na asusun gwamnati domin gina makarantu zuwa wani asusun banki na gidan abinci.

vanguard news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp