Jam’iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da kamawa tare da tsare tsohon gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, lamarin da ta zargi jam’iyyar APC da yunƙurin jefa dimokuraɗiyyar ƙasar cikin ruɗani.
A wata sanarwa sakataren watsa labaran PDP na jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar, ya ce wannan na cikin yunƙurin cin zarafi da murƙushe jam’iyyun adawa a ƙasar.
Ya ce ana wannan kame-kamen ne “a daidai lokacin da aka fara ƙoƙarin samar da haɗakar jam’iyyun adawa a ƙasar domin fuskantar zaɓe mai zuwa,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa kamen ba zai hana komai ba wajen yunƙurin da suke yi na kawo sauyi.
“Muna kira ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ta daina zama karen farauta domin cin zarafin jam’iyyun adawa.”
Tun da farko, Hukumar EFCC ce ta gayyata, sannan ta tsare tsohon gwamnan bisa zarginsa da almundahanar kuɗi.
Rahotanni sun ce sanatan ya isa ofishin hukumar ne da kansa domin amsa gayyatar da aika masa a ranar Litinin, sannan hukumar ta riƙe shi.