fidelitybank

Kallo ya koma sama: ‘Yan barandan siyasa sun daukewa wani jami’i bindiga a taron APC

Date:

Wani dan sandan da ke da alaka da wani dan siyasa ya shiga tsaka mai wuya a lokacin da ‘yan bangar siyasa da ‘yan daba, wadanda suka mamaye dandalin Eagle Square, wurin taron jam’iyyar APC, bayan sun dauke masa bindigar sa ya nema ya rasa.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan barandan suka tilastawa shiga wurin taron. A cewar Sahara Reporters.

‘Yan barandan sun yi amfani da tsarin tsaro inda suka ture shingen, lamarin da ya haifar da hargitsi a wurin taron.

Rikicin da ya biyo baya ya sa mutane da dama suka samu raunuka daban-daban.

A halin da ake ciki kuma, ‘yan sanda sun kama wasu ‘yan daba da dama dauke da wukake, laya da sauran muggan makamai a wurin taron.

Jami’an tsaro da suka hada da jami’an ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence da kuma ma’aikatun gwamnatin tarayya sun bankara barayin.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp