Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da tsohon mai ba shi shawara kuma abokinsa, Elon Musk.
Shugaba Trump ya shaida wa kafar watsa labarai ta NBC cewa Mista Musk zai fuskanci “mummunan sakamako” idan har ya sake ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓen ƴan jam’iyyar Democrat don kalubalantar ƴan majalisar Republican da suka goyi bayan kudurin kashe kuɗinsa, da Elon da ya yi ta caccaka.
A baya dai Trump ya yi barazanar sake duba kwangilolin gwamnati da kamfanonin Mista Musk.
Yawancin ƴan Republican sun nuna goyon bayansu ga Trump.