Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi ƙarin haske kan kalamansa da suka janyo ce-ce-ku-ce kan rikicin da ke gudana tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa.
Ya bayyana cewa ‘mummunar fasarar’ aka yi wa kalmansa.
Guterres ya ce ya kaɗu matuka da yadda ake bayyana kalaman da ya yi a kwamitin tsaro, inda ya ce yana da muhimmanci a gane cewa harin da ƙungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba ba ‘haka kawai’ ne ya faru ba.
Ya ce kalaman nasa ”ba su halasta ayyukan ta’addancin da Hamas ta aikata ba, kuma ya yi Allah wadai da “mummunan ayyukan ta’addanci” na Hamas a Isra’ila.
Ya kuma yi magana game da korafe-korafen al’ummar Falasdinawa, amma ya ce ba za su iya ba da hujjar munanan hare-haren Hamas ba.
Ya ce yana da muhimmanci a daidaita lamarin saboda mutunta waɗanda suka rasa rayukansu da kuma iyalansu.


