fidelitybank

Kakakin majalisa da tsohon sakataren Gwamnati sun ziyarci Wike

Date:

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Honarabul Yakubu Dogara a ranar Asabar sun gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a Fatakwal.

An gudanar da taron sirrin ne a gidan gwamna Wike da ke Rumueprikom, karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Ribas.

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Dogara ya dangana ziyarar ta su ne kan neman gina Najeriya mai dunkulewa.

“Kowa ya yarda da mu cewa, Gwamna Wike na daya daga cikin shugabannin siyasa da ba makawa. A gare mu, neman gina Najeriya ce mai dunkulewa. Don haka, muna jin cewa a matsayin wani ɓangare na tsarin ajandar, ya kamata mu sadu da shi kuma shine dalilin da ya sa muke nan. Kuma ga sauran, ko da yake, watakila nan gaba za mu iya tattauna hakan. “

Hakazalika, tsohon sakataren gwamnatin tarayya Lawsl ya bayyana cewa, ziyarar ta su ita ce ziyarar ‘yan uwantaka da gwamnan jihar Ribas.

“Mun zo ziyarar ɗan’uwanmu. Shi (Wike) dan uwanmu ne. Don haka, a yanzu da kuma, Littafi Mai Tsarki ya umurce ku ku ziyarci juna. Abin da muka yi ke nan.”

Lawal ya ce, hulda da Wike ba ta da alaka da taron da wasu shugabannin Arewa suka yi a Abuja ranar Juma’a.

“A’a, akwai abubuwa da yawa da a duniya kuke buƙatar ziyartar ɗan’uwa, don haka babu ruwanmu da taron da muka yi a Abuja.”

legit ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp