Rundunar sojin Najeriya ta fitar da wata ‘yar makala kunshe da ka’idojin tunkarar harkokin zabe ga sojoji yayin babban zaben shekara mai zuwa.
Kwamandan Cibiyar bunkasa kimiyya, da ilmi da fasaha ta rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Bello Alhaji Tsoho ne ya sanar da haka a birnin Ilorin.
Ya ce tuni rundunar sojojin ta fara wallafa dumbin makalar kan tsare-tsare da ka’idojin aikin da za su yi jagora ga sojoji a lokacin zabe.
Manjo Janar Bello Alhaji ya ce game da batun zaben da ke tafe da kuma harkokin siyasar da suka shafe shi, sojoji tun farko, kwararrun jami’an tsaro ne kuma su gaba daya ba su da jam’iyya.
Ba mu da alaka da wata jam’iyya ko wani da ko ma mene ne na wata jam’iyya, in ji shi, mu namu shi ne tabbatar da ganin an samu kyakkyawan yanayi don ganin an yi zabuka cikin gaskiya da ‘yanci da adalci a 2023.