fidelitybank

Kafofin kasar Amurka da Ingila sun dakatar da aiki a kasar Rasha

Date:

Gidajen talabijin na CNN da ABC da CBS da ke Amurka sun ce sun dakatar da yaɗa shirye-shirye a rasha yayin da aka ƙaddamar da wata doka da za ta hukunta masu yaɗa labaran ƙarya, kamar kamfanin labarai na Rasha TASS ya rawaito.

Tun farko BBC ta ce ta dakatar da aiki a cikin Rasha amma za ta ci gaba da aiki daga wajen ƙasar.

“CBS ta dakatar da watsa labarai daga Rasha yayin da muke ci gaba da duba abubuwan da ke faruwa ga tawagarmu da take can saboda sabuwar dokar da aka kafa a yau,” a cewar CBS.

Shi ma ABC ya ce “sakamakon sabuwar dokar tantancewa a Rasha a yau, wasu daga kafofin yaɗa labarai na Yamma ciki har da ABC sun daina yaɗa labarai daga ƙasar”.

Tun farko CNN ta sanar da dakatar da yaɗa labarai daga Rasha, sai kuma kafar labarai ta Bloomberg ta ce ma’aikatanta sun dakatar da aiki a ƙasar.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp