Shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, a jiya ya bada tabbacin cewa, matatar man Dangote zata fara aiki kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar mulki a shekarar 2023.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Da aka tambaye shi ko yaushe matatar man za ta fara aiki, babban attajirin Afrika ya ce; “Da yardar Allah, Shugaban kasa zai zo ya kaddamar da aikin kafin karshen wa’adinsa.”
A cewarsa, idan matatar ta fara aiki, matatar za ta samar da ayyukan yi tare da samar da karin kudaden haraji wanda gwamnati za ta yi amfani da su wajen bunkasa kasar.
“A nan gaba kadan ana sa ran za su ga karin ayyukan yi, ana sa ran za su kara samun wadata. Muna ci gaba da yin sabbin abubuwa da abubuwa masu kyau, sannan kuma muna ci gaba da biyan harajin da za su taimaka wa kokarin gwamnati na samar da ilimi da lafiya da sauran su,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko ya damu da karancin potassium a sakamakon rikicin Rasha da Ukraine, Dangote ya ce, babu bukatar damuwa domin kashi 26% na arzikin da ake samu a duniya ya fito ne daga kasashen biyu.