Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa, matsalar yan ta’addan Boko Haram za ta kare kafin shugaba Buhari ya miƙa mulki a 2023.
The Nation ta rawaito cewa, Zulum ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati, bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Aso Villa.
Gwamnan ya sanar da cewa, akalla yan ta’adda 30,000 daga ƙungiyar Boko Haram da yar uwarta ISWAP ne suka miƙa wuya ga gwamnatin Najeriya zuwa yanzun.
Haka nan kuma Zulum ya tabbatar da cewa, gwamnatin jihar Borno ba ta sanya wa ‘yan ta’adda wata garabasa ba, domin sun miƙa wuya, inda ya jaddada cewa, suna miƙa wuya ne bisa radin kansu.