Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana fatan ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a daidai lokacin da ake shirin shiga watan Ramadan.
Ana sa ran cewa watan na Ramadana mai alfarma, zai fara ne a ranar 10 ko 11 ga Maris.
Da aka tambaye shi ko yana sa ran cimma yarjejeniya a lokacin, Mista Biden ya ce: “Ina fatan haka. Har yanzu muna aiki tukuru a kan hakan.”
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawa kan tsagaita wuta da kuma ƙara matsin lamba ga Mista Biden da ya taimaka wajen kawo karshen rikicin.
Yarjejeniyar da aka tsara, za ta dakatar da ayyukan soji na tsawon kwanaki 40 tun daga farkon watan Ramadan sannan kuma za a ƙara kai kayan agaji zuwa Gaza, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
An kuma bayar da rahoton cewa yarjejeniyar ta kunshi sakin fursunoni FalasÉ—inawa da kuma sakin Isra’ilawan da ake garkuwa da su.