Kafar yaɗa labarai ta ABC News da ke Amurka ta amince ta biya dala miliyan 15 ga sabon shugaban Amurka mai jiran-gado, Donald Trump bayan da ya kai kafar ƙara a kan zargin ɓata masa suna.
Ya kai ƙarar ne saboda wata hira da mai gabatar da shiri a tashar, George Stephanopoulos, yake cewa an samu shugaban mai jiran-gado da laifin fyade a wata shari’a.
A lokacin wata hira a shirin na talabijin, a watan Maris, hirar da ta yi zafi, inda, George Stephanopoulos da ke tattaunawa da ‘yar majalisar wakilai ta jamiyyar Republican, mai gabatarwar ya rika cewa kotu ta samu Mista Trump da laifin fyaɗe.
Mista Trump ya kai karar tashar talabijin ɗin ta ABC da kuma Mista Stephanopoulos.
Yanzu dai bayanai na nuna cewa ɓangarorin biyu sun sasanta, kuma a ƙarƙashin yarjejeniyar da suka cimma, ABC za ta biya dala miliyan 15, ga wata gidauniyar Trump da kuma wani gidan adana kayan tarihi.
Haka kuma kafar yaɗa labaran za ta biya dala miliyan ɗaya da Mista Trump ɗin ya kashe a sharia’r.
Bugu da ƙari a ƙarƙashin yarjejeniyar sasanton za a sanya wata sanarwa a jikin wata Maƙala da ake rubutawa a shafin intanet na ABC News da ke nuna kafar da George Stephanopoulos na nadamar kalaman da ya yi.