Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya gargadi kafafen yada labarai da kada su jefa Najeriya cikin halin kaka-nika-yi da suka da yawa.
Adesina ya kuma bukaci a ci gaba da hada kai da kafafen yada labarai, domin taimakawa gwamnati da ‘yan kasa su tabbatar da burinsu na Najeriya.
Ya bayyana haka ne a ranar Talata a fadar gwamnati da ke Abuja, lokacin da wani gidan rediyo ya ba shi lambar yabo.
Adesina ya ce: “Ya kamata kafafen yada labarai su hada kai da gwamnati maimakon zama abokan gaba. Abin da za ka samu a kafafen yada labarai a wasu lokuta shi ne cewa suna adawa da gwamnati, wanda ba dole ba ne. Wannan ita ce ƙasarmu kuma ba mu da wata ɗaya.
“Idan har suka jefa kasar nan cikin tsaka mai wuya ta hanyar suka da yawa, ko kafafen yada labarai ma ba za su iya yin aikinsu ba. Don haka ya kamata a ko da yaushe mu tuna cewa kasarmu ce kuma duk abin da muka yi da ita shi ne abin da muke samu.”