Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) ta ce, jihar Kaduna ta bi sahun Jigawa, Nasarawa da Kano wajen yi wa adadin wadanda suka cancanta allurar rigakafin cutar COVID-19 a kullum a kasar.
Dakta Nneka Onu, Darakta, Tsarin Kula da Lafiya a matakin farko, NPHCDA, wanda ya wakilci Babban Darakta, NPHCDA, Dakta Faisal Shuaib, ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja, yayin taron manema labarai na mako biyu na ministocin, sabuntawa kan martanin COVID-19 da ci gaba a cikin bangaren lafiya.
Shuaib ya ce, jihohi biyar da suka hada da Nasarawa da Jigawa da Kano da Kwara da kuma Ogun ne ke kan gaba a matsayin jahohin hukumar da ke kan gaba wajen yaki da cutar COVID-19 a kasar.
“A cikin kwanaki bakwai da suka gabata, jihohin Jigawa da Nasarawa sun inganta yanayin mutanen da aka yi musu allurar da sama da kashi 3.5 da kuma kashi biyar bisa dari.