Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce jihar Kaduna ce ta fi kowacce jiha yawan mutanen da suka yi rajista ta shafin internet daga yankin Arewa.
Kwamishiniyar zabe, Asma’u Maikudi, ta ce jihar mai rajista 486,589, ita ma ta zama na uku a cikin adadin wadanda suka kammala rajistar su.
“Ya zuwa ranar Litinin, 16 ga watan Mayu, jihar Kaduna ta sami mafi yawan masu rajista ta yanar gizo a yankin arewacin Najeriya kuma na uku mafi girma a rajistar jiki,” inji ta.
Misis Maikudi ta danganta wannan ci gaban da hadin kan masu ruwa da tsaki da suka hada da malaman addini da kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin farar hula da kuma kafafen yada labarai.
Sai dai ta ce, duk da wannan abin yabo ne, INEC ta gano cewa, kusan kashi 37.4 na sabuwar rijistar da aka yi a jihar Kaduna ba ta da inganci.