Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, a lokacin da yake kada kuri’arsa a mazabarsa ta Gawuna, ya jaddada kaddarar sa tana hannun Allah.
Gawuna, wanda ya kada kuri’a a cikin daruruwan masu kada kuri’a, ya ce yana da yakinin cewa za a gudanar da zaben cikin lumana tare da cikakken tsaro.
“Iko daga wurin Allah yake kamar yadda na saba fada, kuma ba ni da damuwa ko kadan domin na san Allah ya riga ya kaddara wanda zai ci wannan takara,” inji shi.
Karanta Wannan: Gwamnan Oyo ya jefa kuri’arsa
Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa fitowar masu kada kuri’a ma wani abin alfahari ne domin tun karfe 8 na safe kusan dukkanin rumfunan zabe a Kano an ce masu kada kuri’a ne suka karbe su.
Hakazalika, Dan takarar na APC ya yabawa INEC kan shirye-shiryen da aka yi tun farko da kuma hanzarta jigilar kayayyakin zabe.


