fidelitybank

Ka sauka daga mulki kaiwa Buhari ka gaza – Ƙungiyar Dattawan Arewa

Date:

Ƙungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NEF) ta nemi Shugban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya sauka daga mulki nan take, sakamakon kashe-kashen da ake fama da su a faɗin ƙasar, musamman a arewaci.

Da yake magana cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kakakin ƙungiyar Hakeem Baba-Ahmed, ya ce,Buhari “ba zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabe mu ba”.

“Da alama gwamnatin Buhari ba ta da abin cewa game da ƙalubalen tsaro da muke ciki. Ba zai yiwu mu ci gaba da zama ƙarƙashin ikon masu kisa ba, da masu garkuwa da mutane, da masu fyaɗe, da miyagun da suka hana mu ‘yancinmu na zama lafiya,” a cewar ƙungiyar.

Kiran nasu na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ‘yan bindiga sun kashe kusan mutum 200 a Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, da kuma sace wasu ɗaliban kwaleji mata da aka yi a Jihar Zamfara ranar Talata da dare.

Kazalika, har yanzu ‘yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja na riƙe da gwamman matafiyan da suka yi garkuwa da su, inda suke neman gwamnatin Buhari ta biya musu “buƙatunsu”.

“Kundin tsarin mulkinmu ya tanadi yadda shugabanninmu za su sauka daga mulki idan suka gaza ko kuma saboda wani dalili na ƙashin-kai,” in ji NEF. “Loƙaci ya yi da ya kamata Buhari ya fara tunanin wannan zaɓin.”

punch news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp