fidelitybank

Juyin mulki laifin cin amanar ƙasa ne – Sojoji

Date:

Hedikwatar tsaro (DHQ) ta yi gargadi kan kiraye-kirayen juyin mulkin da sojoji suka yi a Najeriya, inda ta bayyana cewa laifin cin amanar kasa ne.

Gargadin ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda ya bukaci sojojin Najeriya da su karbe mulki daga hannun gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Da yake mayar da martani, rundunar sojin, a wata sanarwa da Daraktan yada labaranta, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Litinin, ta ce, sojojin sun jajirce wajen kiyayewa da ci gaban dimokradiyyar mu, kuma suna biyayya ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar ta kara da cewa sojojin na ci gaba da mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kare mutuncin kasa.

Hukumar ta DHQ ta kuma umurci hukumomin tsaro da abin ya shafa a kasar da su dauki matakin da ya dace a kan duk wani mutum ko kungiyar da ke yin kira ga sauye-sauyen da ba su dace ba a kasar.

legit.ng.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...
X whatsapp