Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta ta kori kocinta Massimiliano Allegri kwana biyu bayan ya jagoranci ‘yan wasanta sun lashe kofin gasar Coppa Italia.
Juve ta doke Atalanta 1-0 a birnin Rome, amma an bai wa Allegri jan kati saboda hayagaga da ya yi wa alƙalan wasa.
Tuni mahukuntan gasar ƙwallon Italiya suka ƙaddamar da bincike a kan Mista Allegri.
“Korar ta biyo bayan wasu ɗabi’u a lokacin da kuma bayan tashi daga wasan Coppa Italia wanda kulob ɗin ke ganin sun saɓa da al’adun Juventus,” a cewar sanarwar da kulob ɗin ya fitar.
Nasarar lashe kofin a ranar Talata ta sa Allegri ya kafa tarihin cin kofin har sau biyar a matsayin mai horarwa.