Kungiyar kwallon kafa ta Seria A, Juventus na zawarcin dan wasan tsakiya na Leicester City, Wilfred Ndidi a wannan bazarar.
Ndidi yana cikin watannin karshe na kwantiraginsa da Leicester City kuma zai iya barin kungiyar a kyauta a karshen wata.
A cewar Tuttosport, dan wasan na Najeriya yana cikin ‘yan wasa uku da Juventus ke neman siyan dan wasan tsakiyarta a bazara.
Sauran ‘yan wasan biyu su ne Jorginho da Mikel Merino.
Rahotanni sun nuna cewa Ndidi yana da sha’awar kungiyoyi a Ingila, Spain da kuma Turkiyya.
Dan wasan mai shekaru 27 ya yi rajistar kwallaye hudu kuma ya taimaka a wasanni 32 da ya buga wa Leicester City a kakar bana.J