A daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke bikin ranar dimokradiyyar kasar nan, ranar 12 ga watan Yuni, wasu da suka fusata a jihar Legas sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da halin da kasar ke ciki.
Masu zanga-zangar da suka taru a Ikeja, sun ce lokaci ya yi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ya kamata ta sauka daga kan mulki.
Al’umma dai sun fito kan tituna suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da yunwa da tabarbarewar tattalin arziki da ake fuskanta.
Sun bayyana bukatarsu ne kan matsalar tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, inda suka jaddada cewa “’yan Najeriya ba za su iya ciyar da iyalansu cikin kwanciyar hankali karkashin Tinubu ba.
Rahotanni na cewa, masu zanga-zangar sun daga kwalaye masu dauke da sakwanni irin su, ‘Shugaba Tinubu, ka bar marasa galihu su shaki iska, kuma sun a jin yunwa.
Hakazalika, a Abuja, ‘yan Najeriya da suka fusata sun taru a karkashin gadar Berger domin nuna adawa da gwamnatin Tinubu.