Fitaccen ɗan wasan damben Birtaniyar nan, Anthony Joshua, ya doke dan wasan damben nan dan asalin Kamaru, Francis Ngannou a fafatawar da suka a ƙasar Sadiyya.
Joshua, mai shekara 34, ya doke Francis Ngannou a turmin farko da na biyu da suka fafata ranar Juma’a.
Dan wasan na Kamaru mai shekara 37 ya sha kashi ne a lokacin karawar tasu, inda har ya buƙaci kulawar lafiya.
Karawar Joshua da Ngannou dai wani zakaran gwajin dafi ne kan abin da zai faru tsakanin sa da Fury, kuma nasarar da Joshuan ya samu wata manuniya ce ta fatan ƙara tabbata gwarzo a wasan damben Birtaniya.
A watan Disamba Joshua ya doke Otta Wallin, ɗan ƙasar Sweden ɗin da ya zamo wa Tyson Fury ƙarfen ƙafa a tsawon shekara huɗu.
Za a ɗauki lokaci mai tsawo duniyar damben zamani ba ta manta da gwarazan da suka fafata a fagen daga kamar Tyson Fury da Anthony Joshua ba, musamman ta la’akari da yadda sunayen su suka zamo tamkar wani suna ne na wasan damben.