Ƙasar Jordan ta ɗauki matakin da ta kira martaninta kan yaƙin da Isra’ila take yi a Zirin Gaza ta hanyar janye jakadanta daga Isra’ila.
Wata sanarwa ta ce Mataimakin Firaminista kuma Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ne ya ba da umarnin janye jakadan “don nuna ɓacin ran Jordan kan tashin hankalin da ke faruwa a Gaza”.
Ranar Lahadin da ta wuce, Safadi ya faɗa wa BBC yayin wata hira cewa Jordan “za ta yi duk abin da za ta iya a lokacin da ya dace, duk abin da muke ganin zai taimaka a yaƙin nan, za mu yi shi”.
Jordan ce ƙasar Larabawa ta farko da ta ɗauki irin wannan mataki.
Kamar Masar, wadda ita ma ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila, har ma da wasu Larabawan da suka gyara alaƙa da ita, Jordan na da ofishin jakadanci a birnin Tel Aviv na Isra’ila.
Haka nan ƙasar ta faɗ wa jakadan Isra’ila, wanda ya bar birnin Amman mako biyu da suka wuce saboda zanga-zanga, cewa kada ya koma.
Sanarwar ta Jordan ta fayyace cewa komawar jakadan Isra’ila ƙasar “ya dogara ne idan yadda Isra’ilar ta dakatar da hare-hare a Gaza”.
Ta kuma bayyana damuwarta kan “matsananciyar rayuwa da ake ciki” a Gaza.