A ranar Alhamis din da ta gabata ne tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bukaci daukacin ‘yan takara a zaben 2023 da suka hada da irin su Peter Obi, Atiku Abubakar, da Bola Tinubu, da dai sauran su da su yi kokarin ganin yakin neman zabensu ya kasance mai tsafta kuma babu tashin hankali.
Jonathan ya yi wannan kiran ne a sakon sa na fatan alheri da aka karanta a Abuja a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa kan zaben 2023 na farko, wanda ya samu halartar ‘yan takarar shugaban kasa da jam’iyyunsu.
Ya kuma yi kira ga ’yan takara da masu tallata su da magoya bayansu da su jajirce tare da gudanar da yakin neman zabensu kan batutuwan da suka shafi ‘yan Najeriya.
Jonathan ya ce, “Muna kan wani muhimmin mataki a rayuwarmu ta kasa inda ba mu da wani zabi illa inganta hadin kan kasa, soyayya da fata domin samun ci gaban da ake bukata.
“Ba za mu iya ci gaba da wasa da siyasar ɗaci da rarrabuwar kawuna ta kabilanci da addini ba. Domin irin wannan siyasar tana nuna babban hatsari ga hadin kanmu, ci gabanmu da wadatar dimokuradiyyarmu.
“Dole ne mu yi la’akari da illar kalaman kyama, labaran karya da farfaganda marasa tunani, musamman a wani yanayi da ya kamata a karfafa tsarin hadin kai da kwanciyar hankali.
“Ina kira ga ’yan takara da masu tallata su da magoya bayansu da su jajirce tare da neman gudanar da yakin neman zabensu kan batutuwan da suka shafi jama’armu.
“Ya kamata, ta kowane hali, su guje wa hare-haren da ba dole ba a kan mutane, da kuma amfani da kalaman batanci ga wadancan abubuwan da ke haifar da hargitsi da rikici a lokacin zabe.”