Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya sauka a kasar Zimbabwe gabanin babban zaben kasar.
A ranar 23 ga watan Agusta ne al’ummar Zimbabwe za su kada kuri’a domin zaben sabbin shugabanni.
Jonathan, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar, ya ce, ya isa Harare ne a ranar Asabar din da ta gabata gabanin zaben.
Tsohon shugaban kasar ya ce, ya jagoranci sauran mambobin kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta AU, da kungiyar hadaka ta hadin gwiwa ta kasashen gabashin Afirka (COMESA) zuwa kasar Zimbabwe, domin halartar zaben; yana jaddada cewa yana fatan samun kwarewa mai gamsarwa.
“Ina godiya ga gwamnatin Zimbabwe, AU da COMESA da kuma Ambasada Zachariah Ifu da sauran jami’an hukumar ta Najeriya, bisa kyakkyawar tarba,” in ji shi.