Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya roki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya mara masa baya domin sake tsayawa takara a 2015.
Wike, ya bayyana cewa Atiku ya ki amincewa da rokon da Jonathan ya yi na ya goyi bayan sake tsayawa takara.
Gwamnan ya yi magana ne a lokacin da Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya kaddamar da hanyar Akpabu-Itu-Umudiogha a karamar hukumar Emohua ta Rivers.
Wike ya ce: “Jonathan ya yi tafiya zuwa otal din Dorchester da ke Landan don ganawa da Atiku, amma tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce Jonathan ya bar masa tikitin takara a 2015.”
Jonathan wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a shekarar 2015, ya sha kaye a zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A halin da ake ciki, Atiku da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa, sun ziyarci Jonathan kwanakin baya.
Ziyarar dai ba ta rasa nasaba da rikicin da ya addabi jam’iyyar PDP.
Wike dai yana takun saka tsakaninsa da Atiku da shugabancin jam’iyyar tun bayan da ya sha kaye a yunkurinsa na zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.