Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya je kasar Kenya domin sa ido kan yadda zaben kasar ke gudana.
Mr Jonathan ya je ƙasar ne a karkashin inuwar wata kungiyar lura da zabe da manazartan dauwamammiyar dimokradiyya a Afirka (EISA), a matsayin dan kungiyar, domin gani-da-ido na yadda zabe ke tafiya a wasu mazaɓu a birnin Nairobi da ke Kenya. In ji BBC.
Shugaban ya bayyana manufar ziyarar a shafinsa na Facebook da cewa “yayin da mutanen Kenya suka fito yau domin jefa kuri’a a duk faɗin ƙasar, muna sa ran za a fito da sakamakon zaɓe lafiya da kuma karfafa dimokradiyyar ƙasar Kenya.