Wakilin Kyaftin din Argentina, Lionel Messi wato Marcelo Mendez, ya yi watsi da rade-radin cewa, abokin cinikin nasa na gab da shiga Inter Miami lokacin da kwantiraginsa da Paris Saint-Germain za ta kare a bazara mai zuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa Messi wanda ya zaburar da Argentina ta doke Mexico da ci 2-0 a gasar cin kofin duniya da aka buga a karshen makon da ya gabata, zai bar PSG a matsayin kyauta.
Da yake mayar da martani ga hasashe, Mendez ya sanya jita-jita ‘labaran karya’.
“Karya ce,” Mendez ya gaya wa CNN lokacin da aka tambaye shi game da rahotannin. “Labarin karya ne.
“Babu wata tattaunawa don Lionel ya koma Inter Miami kakar wasa mai zuwa.”
Duk da musantawar Mendez, Inter Miami ta kasance É—aya daga cikin waÉ—anda aka fi so don siyan Messi, wanda ya riga ya mallaki gida a cikin birni kuma ya yi hutu a lokuta daban-daban tare da danginsa.