Jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya faɗi a ranar Talata da safe.
Lamarin dai ya jefa fargaba a tsakanin fasinjoji da ke cikin jirgin.
Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a kauyen Asham da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma jirgin ƙasa ta bar Abuja ne da misalin karfe 9:45.
Har yanzu ba a san abin da ya jawo saukar jirgin daga kan layin dogo ba, kuma babu tabbacin ko an samu waɗanda suka jikkata.
Hukumar Jiragin ƙasar Najeriya (NRC) bata yi tsokaci ba a kan lamarin.