Wani jirgin ruwan yaƙin Birtaniya, HMS Trent, ya sauka a Lagos don taimakawa wajen yaƙi da haramtattun ayyuka ciki har da fashin teku da fasa-ƙwauri a tsakanin ƙasashen yankin.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya ya fitar, ta ce wannan karo na biyu da jirgin yaƙin Trent ke kawo ziyara Najeriya.
“Ziyarar za ta taimaka wajen bunƙasa samar da horo da tallafa wa tsaron teku a yankin mashigin tekun Guinea,” kamar yadda sanarwar ta ce.
Jirgin HMS Trent ya baro Gibraltar ɗauke da wani rukunin ƙwararrun sojojin ƙundumbalar Birtaniya da wani jirgi maras matuƙi da ke aikin tattara bayanai mai suna Puma. Aikin jirgin HMS Trent shi ne ya tallafa wa Ƙasashen Afirka ta Yamma abokan ƙawancen Birtaniya wajen inganta ƙwazo kan yaƙi da laifuka a teku da kuma tabbatar da kawo ƙarin kwanciyar hankali a faɗin yankin.
Da harkokin kasuwancin fam biliyan shida na Birtaniya da ke wucewa ta yankin, wani ɓangare na aikin Trent shi ne tallafa wa ayyukan kwanciyar hankali a Mashigin Tekun Guinea ta hanyar ba da horo don taimaka wa rundunonin sojin ruwan ƙasashe abokan ƙawance, su kai yaƙi ga masu aikata laifi da kyautata ƙawance da musayar ilmi a lokacin da suke sintiri don ƙara tabbatar da tsaro.
Babban kwamandan jirgin ruwan HMS Trent, Kwamanda Tim Langford, ya ce, “wata karramawa ce ga jirgin yaƙin HMS TRENT ya sake komo wa Najeriya, wannan wata muhimmiyar ziyara ce ga aikin da aka turo jirgin ruwan zuwa Afirka ta Yamma tsawon wata uku”.
Mataimakin Babban Jakadan Birtaniya a Najeriya, Jonny Baxter ya ce, “Turo wannan jirgin ruwan yaƙi zuwa Afirka ta Yamma wata manuniya ce kan yadda Birtaniya ke daɗa bayar da himma a matakin harkokin duniya wajen shawo kan ƙalubalen tsaro.


