Rahotanni na cewa wani jirgin sama na kasar Ukraine ya fado a kudancin kasar kuma hukumomi sun ce, akai wadanda suka rasa rayukansu.
Jirgin samfurin AN-26 ne mai jigilar kayan soji da rundunar sojojin kasar Ukraine ke amfani da shi.
Ya fado da safiyar yau Juma’a gundumar Vilnia na lardin Zaporizhzhia.
Hukumomin sojojin kasar sun ce ana binciken hadarin.